Connect with us

News

Wasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Motar Yan KAROTA A Kano

Published

on

Screenshot 20260805 191618 Facebook 750x430

Jami’ai uku na Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) sun jikkata bayan wasu fusatattun matasa sun kai musu hari tare da ƙona motar sintirin hukumar, bayan wani hatsari da ya faru a Kwanar Dawaki da ke kan titin Zariya a Kano.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne lokacin da jami’an KAROTA suka tsayar da wata motar haya domin duba takardunta da kuma tabbatar da bin dokokin hanya. A yayin binciken ne wata babbar mota (trailer) da ake zargin tana tafiya da gudun wuce kima ta bugi motar hayar.

EFCC Ta Dakatar Da Asusun Gwamnatin Osun Ne Kan Zargin Almundahanar Miliyoyin Naira

Mataimakin shugaban tawagar sintirin KAROTA da ke titin Zariya, Ibrahim Abubakar Ibrahim, ya ce fasinjoji da dama sun samu raunuka, inda jami’an hukumar suka fara aikin ceto tare da kai waɗanda suka jikkata asibiti.

Ya ce yayin da jami’an ke ƙoƙarin ceton waɗanda hatsarin ya rutsa da su, wasu fusatattun matasa sun zargi KAROTA da haddasa hatsarin, suka kai musu hari. A sakamakon haka, jami’ai uku sun jikkata, sannan aka ƙona motar sintirin hukumar.

An kuma ce direban babbar motar da ake zargin ya haddasa hatsarin ya tsere daga wurin kafin a kama shi.

Advertisement

Da yake martani kan lamarin, Manajan Daraktan KAROTA, Faisal Mahmud Kabir, ya yi kira ga al’umma da su rika mutunta jami’an da ke gudanar da ayyukansu bisa doka, yana mai cewa aikinsu shi ne tabbatar da tsaro da daidaita zirga-zirga a kan hanyoyin jihar

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na KAROTA, Abubakar Ibrahim Sharada, ya sanya wa hannu, hukumar ta yaba da jajircewar jami’anta duk da irin ƙalubalen da suke fuskanta wajen gudanar da aikinsu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending