Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutune 17 Bisa Zargin Aikata Laifuka Daban-daban A Jigawa

Published

on

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta kama mutum 17 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da satar shanu, fasa shaguna da lalata kayayyaki.

Kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne yayin samamen da jami’an ’yan sanda suka gudanar a wasu ƙananan hukumomi 11 na jihar.

KADUNA: Jami’an Ƴansanda Sun Tarwatsa Sansanonin Ƴan Bindiga A Makarfi

Ƙananan hukumomin sun haɗa da Malam Madori, Gwaram, Garki, Kiyawa, Taura, Birniwa, Dutse, Ringim, Miga, Kazaure da Roni.

A yayin samamen, ’yan sanda sun ƙwato babura biyar, shanu biyar, awaki biyu da tunkiya ɗaya.

Haka kuma sun ƙwato wayoyi ƙirar Android tara, batura 44, layin waya guda huɗu da kwamfuta guda ɗaya.

Advertisement

Sauran kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da talabijin, batirin sola, fanka da wasu kayan da ake zargin na sata ne.

Rundunar ta ce samamen sun biyo bayan bayanan sirri da kuma binciken da jami’anta suka gudanar.

A wani samame kuma, an kama mutane uku da ake zargi da hannu wajen satar babur ƙirar Boxer wanda darajarsa ta kai Naira miliyan 1.2.

Sai dai har yanzu ba a gano baburi ɗin ba.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano masu kayayyakin da aka ƙwato domin mayar musu kayansu bisa doka.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Tijjani Murtala, ya ce rundunar za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri domin daƙile laifuka.

Advertisement

Ya gargaɗi masu aikata laifuka da masu taimaka musu da su daina, yana mai cewa rundunar za ta tabbatar da gurfanar da masu karya doka a gaban kotu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending