Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Kuɓutar Da Mutane 23  Da Aka Yi Garkuwa Da Su A  Zamfara

Published

on

WhatsApp Image 2026 09 04 at 15.13.41

Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun kuɓutar da mutane 23 da aka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara, tare da dakile wani yunƙurin satar mutane a Ƙaramar Hukumar Bungudu.

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarun sun kuɓutar da mutanen ne yayin wani sintiri a wajen garin Wuya, Ƙaramar Hukumar Anka.

Mutane Uku Sun Mutu Yayin Da Wata Mota Ta Fado Daga Gadar Da Ke Kan Titin Lagos Zuwa Ibadan ‎

Mutanen sun ƙunshi maza uku da mata 20, waɗanda aka sace daga Ƙaramar Hukumar Gummi kuma suka shafe kusan makonni uku a hannun masu garkuwa da su.

Rundunar ta ce ana ba su kulawar lafiya kafin a mayar da su ga iyalansu.

A Bungudu kuma, dakarun sun dakile yunƙurin ’yan bindiga na yin garkuwa da mazauna Dankurmi, bayan sun yi musayar wuta da su.

Advertisement

Sojojin sun ce ’yan bindigar sun tsere ne bayan sun sha ƙarfi, yayin da aka gano alamun jini a hanyar da suka bi, wanda ke nuna cewa wasu daga cikinsu sun samu raunuka.

Rundunar ta ce tana ci gaba da farautar ’yan bindigar domin tabbatar da tsaron al’ummomin yankin.

 

 

PRNIGERIA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending