Connect with us

News

lyalan Daliban Borno 80 Da Aka Sace Sun Yi Barazanar Zuwa Fadar Shugaban Ƙasa “Aso Rock”

Published

on

Aso Rock Villa 768x476
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Iyalan ɗalibai 80 da aka yi garkuwa da su a yankunan Mussa da Lassa, cikin ƙaramar hukumar Askira/Uba ta Jihar Borno, sun yi barazanar zuwa Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja cikin kwanaki shida, muddin ba a sako ’ya’yansu ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Yaran sun shafe sama da kwanaki 130 a hannun masu garkuwa Mutane, bayan da aka sace su a ranar 15 ga Mayun 2026.

An Kama Mai PoS da Ake Zargi Da Taimakon Mai Garkuwa Da Mutane A Katsina 

A cewar iyalan, daga cikin yaran akwai 44 da aka sace daga Mussa da kuma 36 daga Lassa.

Iyalan sun bayyana hakan ne yayin wata zanga-zanga da suka gudanar a Askira/Uba, inda suka nuna damuwa kan abin da suka bayyana a matsayin jinkirin da hukumomi suka yi wajen ceto yaran.

Shugaban iyayen, Ishaku Suya, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya taimaka wajen ceto yaran.

Advertisement

Suya ya ce iyayen za su nufi Fadar Shugaban Ƙasa idan ba a ceto ’ya’yansu cikin kwanaki shida ba.

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar yankin, Midala Usman Balami, ya kuma ce ya taba gabatar da batun a Majalisar Wakilai, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Borno su yi amfani da dukkan hanyoyin tsaro wajen ceto yaran.

Ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto, Fadar Shugaban Ƙasa ba ta fitar da sanarwa kan barazanar iyalan ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending