Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina

Published

on

FB IMG 1790083304888

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto ɗalibai mata shida na Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma, tare da wani direban mota, bayan ’yan bindiga sun yi garkuwa da su a Jihar Katsina.

Rundunar ta ce an ceto mutanen bakwai ne a wani samame da dakarun Operation FANSAN YAMMA, Sashe na Biyu, suka gudanar.

Cikar Oluremi Tinubu Shekaru 66 Alheri Ne Ga Wa’adin Shugaba Tinubu Na Biyu – Kwankwaso

Lamarin ya faru ne a hanyar Daye zuwa Malumfashi, a Ƙaramar Hukumar Danmusa, bayan ’yan bindigar sun kai hari kan wata motar kasuwanci da ke tafiya daga Kaduna zuwa Katsina.

Bayan samun kiran neman agaji, dakarun sojin sun isa wurin cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta wa ’yan bindigar tserewa zuwa cikin daji, inda suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.

Daga cikin waɗanda aka ceto akwai ɗalibai mata shida na Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma da direban motar.

Advertisement

Sai dai rundunar ba ta bayyana ko an kama wani daga cikin waɗanda ake zargi da hannu a garkuwar ba.

Sojojin sun ce suna ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a yankin domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da dakile ayyukan ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

 

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending