Connect with us

News

Majalisar Dokokin Rivers Ta Amince Da Kudurin Dokar Kirkiro Ƴansandan Jihohi

Published

on

Rivers Assembly 1784031230 768x320

Majalisar dokokin jihar Rivers ta amince da ƙudurin dokar kafa ƴan sandan jihohi da majalisar tarayya ta aike mata domin yin duba a kai.

Ƙudurin dokar dai ya buƙaci da a yi gyara cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, domin yin dokar da za ta amince da ƙirƙiro ƴan sandan jiha tare kuma da ci gaba da riƙe ƴan sandan Najeriya a matakin ƙasa.

Pantami Ya Lashe Sabon Zaɓen Dan Takarar Gwamnan Gombe A Jam’iyyar PDP

A zaman majalisar dokokin jihar Rivers ɗin na jiya Litinin ta amince da ƙudurin gyaran dokokin guda shida na shekarar 2026, inda ta zama jiha ta uku da ta amince da ƙudurin dokar bayan jihohin Osun da Edo.

Da yake jawabi kafin gabatar da ƙudurin domin yin zaɓe a kai, Kakakin Mjalisar Martin Amaewhule, ya bayyana buƙatar samar da ƴan sandan jihar domin tsare ƴan ƙasa da hakkokinsu da kuma samun bayanan aikata laifuka.

Cikin wata sanarwa da mataimaki ga kakakin majalisar Martins Wachukwu ya fitar, ya ce ƴan majaliar sun kaɗa ƙuri’un bai ɗaya wajen amincewa da ƙudurin dokar, ya kuma yi kira da a samar da matakan da za su hana gurɓata tsarin.

Advertisement

 

 

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending