News
An Rantsar Da Alƙalai 375 Domin Sauraron Ƙararrakin Zaɓen 2027

An rantsar da alƙalai 375 da za su yi aiki a kotunan sauraron ƙararrakin zaɓen 2027 a Najeriya, gabanin babban zaɓen da ake sa ran gudanarwa a ƙasar.
An gudanar da bikin rantsar da alƙalan ne ranar Litinin a harabar Body of Benchers da ke Abuja, yayin wani taron horas da su kan shari’o’in zaɓe.
Wasu Bata Gari Sun Kwance Fanka 25 A Wani Masallaci A Kano
Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta ce rantsar da alƙalan wani muhimmin mataki ne na shirya ɓangaren shari’a domin tunkarar ƙararrakin da za su taso bayan zaɓen 2027.
Ta bayyana cewa ingancin dimokuraɗiyya ba ya ta’allaka ga yadda ake gudanar da zaɓe kawai, har ma da kasancewar tsarin shari’a mai zaman kansa, adalci da kuma hanzarin warware takaddamar zaɓe.
A cewarta, kotuna na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen kare zaɓin al’umma, tabbatar da bin kundin tsarin mulki da kuma ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin dimokuraɗiyya.
Ta buƙaci alƙalan da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, riƙon amana da adalci, ba tare da nuna son kai ba, tana mai cewa al’umma za ta sa ido sosai kan yadda za su gudanar da shari’o’in.
Dongban-Mensem ta bayyana cewa an zaɓo alƙalan ne daga kotuna da hukumomin shari’a daban-daban a faɗin ƙasar.
Ta ce daga cikin alƙalan 375, guda 138 sun taɓa zama mambobin kotunan sauraron ƙararrakin zaɓe a baya, yayin da sauran 237 za su fara gudanar da irin wannan aiki.
Rantsar da alƙalan ya yi daidai da sashe na 285 (1) da (2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, wanda aka yi wa kwaskwarima, wanda ya bai wa Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara ikon kafa kotunan sauraron ƙararrakin zaɓen Majalisar Dokoki ta Ƙasa, majalisun dokokin jihohi da na gwamnonin jihohi.
Haka kuma, sashe na 134 (3) (a) da (b) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya tanadi wa’adin kafa kotunan da kuma buɗe ofisoshinsu domin karɓar ƙararrakin zaɓe.
A nata ɓangaren, Babbar Alƙaliyar Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta buƙaci alƙalan da su yi aiki bisa doka da ƙa’ida, ba tare da tsoron barazana ko shiga ƙarƙashin tasirin siyasa ba.
Ta kuma gargaɗi ’yan siyasa, lauyoyi, jam’iyyun siyasa da kafafen yaɗa labarai da su guji duk wani yunƙuri na tsoratar da alƙalai ko yin tasiri ga shari’o’in zaɓe.
Babbar Alƙaliyar ta jaddada muhimmancin tabbatar da cewa an yi wa kowane ɓangare adalci, domin kiyaye martabar ɓangaren shari’a da amincewar jama’a da sakamakon shari’o’in zaɓe.
