Connect with us

News

ASUU ta buƙaci a fito da ƙudurin doka kan yawan kai ƴaƴan ƴan siyasa karatu ƙasashen waje

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, ta yi kira da a samar da kudirin doka da zai tsara yadda jami’an gwamnati ke kai ƴaƴan su makarantun da ke ƙasashen waje.

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN ta zabi sabon shugaba

Advertisement

Shugaban Jami’ar ƙungiyar na jami’ar Niger Delta, Wilberforce Island, Farfesa Kingdom Tombra ne ya bayyana haka a wata zanga-zangar hadin kai da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta shirya a jiya Talata a Yenagoa.

Kungiyar NLC ta gudanar da zanga-zangar ne a fadin kasar nan domin nuna goyon bayanta ga kungiyar ASUU da sauran kungiyoyin da ke da alaka da yajin aikin jami’o’in gwamnati a Najeriya.

Advertisement

“Idan aka yi haka, za a gina al’umma ta gari ta hanyar bunkasa manyan cibiyoyin ilimi da inganta kuɗaɗe na tsarin jami’a a Najeriya.

“Wannan gwagwarmayar ba ta adawa da gwamnati ba ce, a’a ta bangaren ma’aikata ga masu mulki, kuma mun jajirce sosai

Advertisement

“Idan masu hannu da shuni su na kai ƴaƴan su jami’a ko cibiya daya, ba na jin za a sake yajin aikin.

“Idan sun yi makaranta a nan kuma ‘ya’yansu suna nan za su nuna cikakken goyon baya ga tsarin jami’a da kuma manyan makarantun Najeriya,” in ji shi

Advertisement

 

 

Advertisement

 

DAILY NIGERIAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending