News
Ganduje zai miƙa sunayen sabbin kwamishinoni gaban majalisar dokoki domin tantance wa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace nan bada jimawa ba zai mikawa majalisar dokokin jihar Kano sunayen sabbin kwamishinoni domin tantancewa.
Yace zai miƙa wa majalisar sunayen sabbin kwamishinonin ne domin maye gurbin tsaffin kwamishinonin da suka samu takara a matakai daban-daban a jam’iyyar APC.
ASUU ta buƙaci a fito da ƙudurin doka kan yawan kai ƴaƴan ƴan siyasa karatu ƙasashen waje
Ganduje ya bayyana hakan ne yayin taron Majalisar zartaswar na mako-mako, wanda aka gudanar a zauren taron Majalisar dake gidan gwamnatin Kano.
” Kamar yadda kuka sani akwai wasu daga cikin ƴan wannan majalisar da suka sami takara a jam’iyyar APC, don haka dole mu maye gurabensu da sabbi don cigaban jihar Kano “. Inji Ganduje
Kimanin kwamishinonin 8 ne suka ajiye aikinsu domin yin takara a jam’iyyar APC a babban zabe mai zuwa na 2023.
DAILY NIGERIAN
