Connect with us

News

Kamfanonin mai na cin kazamar riba a kan talakawa – MDD

Published

on

DAGA SULAIMAN ADO AHMED 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

 

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce bai dace ba sam-sam kamfanonin mai da iskar su rika cin kazamar riba a kan mutanen da suka fi talauci a duniya kuma suna matukar gurbata yanayi.

Da yake gabatar da rahoto a kan matsalar karancin makamashi da ake fama da ita a duniya, Mista Guterres ya bukaci dukkanin gwamnatoci su rika tatsar kamfanoni haraji mai yawan gaske, sannan su yi amfani da kudin wajen taimaka wa mafiya rauni a cikin al’umma.

Chelsea ta fara tattaunawa da Barcelona kan De Jong, Spurs na son Udogie

Ya ce manyan kamfanoni sun ci riba jumulla wadda ta kai kusan ta dala biliyan dari daya a watanni uku na farkon shekarar nan.

Advertisement

Mista Guterres ya zargi kamfanonin man da masu ba su kudaden gudanarwa da tsabar hadamar da ke muzguna wa talakawa, suna kuma lalata muhalli.

Haka kuma ya yi kira ga kasashe da su dauki matakan rage amfani da makamashi mai gurbata yanayi, a madadinsa su hanzarta sauyawa zuwa ga makamashi maras illa ga muhalli.

 

 

BBC NEWS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending