Connect with us

Opinion

Sai al’umma ta yi tunani mai kyau sannan za yi rayuwa mai inganci

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Idan ba sauya yanda kake kallon al’amura ka yi ba to zai yi wuya ka iya sauya kanka. Ma’ana tunanin ka dole sai ya sauya kafin halayyarka ta sauya. Ita kuma halayya tana sauyawa, ko ta yi kyau ko ta munana, saboda tunanin da ke cikin zuciyarka.

Wanda ke ganin gabadayan manufarsa ita ce ya yi kudi kawai ko ta halin kaka, to za ka ga zai iya yin komai, ciki har da kisan kai da sauran miyagun ayyuka, domin samun biyan bukatarsa. Ba ruwansa da abu ya halatta ko ya haramta a gare shi.

Advertisement

Wanda ya fahimci samun kudi wajibi ne, amma shi kudin ba shi ne ainihin matukar abin da yake nema ba, amfanin da zai yi da kudin domin cim ma manufarsa shi ne yake ingiza shi zuwa neman kudin, to za ka ga yana da taka-tsantsan wajen neman kudin da kuma taka-tsantsan wajen abin da zai ci karo da mutuncinsa da addininsa.

Wanda ya yarda Allah ne Yake bayarwa ta hanyar bin sababi, za ka same shi yana da kokari kwarai wajen bin sababin kuma zuciyarsa cike take da yarda “thiqah” cewa Allah din zai ba shi.

Advertisement

Wanda yake jin ko ya nema ko bai nema ba zai samu, tun da an rubuta masa iya arzikinsa, to za ka same shi da kasala da rayuwar kunci, saboda ya yi wa addini mummunar fassarar da ta sabawa ta Annabi da sahabbai.

Wanda ya dauka cewa duniya kazanta ce kuma duk mai kudi wuta zai shiga, za ka same shi tutur cikin talauci da jin haushin wadanda suka nema suka samu.

Advertisement

Wanda ya dauki cewa halal ta yi wuya a yanzu, za ka same shi yana dulmuya cikin nema da cin haram. Ko kuma ka same shi yana jin haushin duk mai kudi da wanda Allah Ya buda wa.

Wanda ya dauki cewa halal ta ma fi saukin samu a kan haram to za ka same shi cikin walwala da neman halal, kuma zai iya hakura da haram komai yawanta.

Advertisement

Duk hanyar da za ta kawo maka kudin gangan, irin kudin sata ko na damfara ko na bati ko na kyauta da iyaye ko yayye da sauransu, to ba sa dawwama. Nemi sana’a ko kasuwanci ko wani aiki.

Ba iya neman kudi kawai wannan ya tsaya ba. Duk yanda kake kallon abu to haka zai zo maka. Idan ka ga kana ta samun matsala, a ko mene ne, to ka tsaya tsam ka dubi gaba da baya. Ka dubi fuskoki da yawa na wannan abin tare da samar da dabarun da za ka bi ka magance su.

Advertisement

Da yawa muna tare da maganin matsalolinmu, amma ba mu gane ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending