Sports
Federer ya sanar da yin murabus da ga wasan Tennis
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shahararren dan wasan Tennis ɗin nan, Roger Federer, a yau Alhamis ya sanar da yin ritaya daga buga wasanni bayan kammala gasar cin kofin Laver mai zuwa.
Federer, wanda ya lashe kyautar Grand Slam sau 20, wanda magoya baya da dama ke ganin shi a matsayin zakaran ƴan wasan tennis na maza, ya kasance yana jiyya tsawon kakar wasan nan bayan tiyatar gwiwa da a ka yi masa.
Yan bindiga sun kai hari Batagawara a jihar Katsina in da suka sace mutane fiye da 50
Amma ana sa ran dan shekaru 41 zai yi murabus a 2023.
Sanarwar tasa na zuwa ne makonni kaɗan bayan da ƴar wasan tennis ta mata, Serena Williams ita ma ta sanar da murabus ɗin ta.
Federer ya ƙara da cewa: “Ni dan shekara 41 ne. Na buga wasanni sama da 1,500 sama da shekaru 24.
“Tennis ya min komai, fiye da yadda nake mafarki, kuma yanzu dole ne in gane lokacin da ya kamata in kawo ƙarshen sana’ata.”
A shekarar 2018 ne a gasar Australian Open Federer ya lashe kyautar Grand Slam ɗin sa ta karshe.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
