News
Gobara Ta Kashe Mutum 9, An Ceto 72 A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ceto rayuka 72 da dukiyoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 38.6 a gobara a watan Satumba.
Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya ce mutane tara ne suka rasa rayukansu a gobara 17 da ta ta lakume dukiyoyin da kimarsu ta kai Naira miliyan 14.8 da ta afku a cikin watan.
Hajj 2022: Gwamnaptin Zamfara ta mayar wa alhazai 1,318 naira 50,000 kowanne
A bayaninsa na ranar Talata a Kano, Alhaji Saminu ya ce, hukumar ta amsa kiraye-kirayen gaggawa guda 49, sannan ta samu kirayen-kirayen nema agajin karya 11 tsawon lokacin.
Ya bukaci jama’ar jihar da su kasance masu taka-tsansan da wuta sannan a i kira ga masu ababen hawa da su kiyaye dokokin hanya domin guje wa hadurra, musamman a lokacin damina.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
