Connect with us

News

An Dakata Da Aikin Titin Abuja-kano Saboda Rashin Tsaro Inji Gwamnatin Tarayya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

 

Gwamnatin tarayya, ta ce gyaran hanyar Abuja zuwa Kaduna da Kano da ake yi ya tsaya ne sakamakon barazanar da ake fuskanta ta rashin tsaro a yankin arewa.

 

Advertisement

Karamin Ministan ayyuka da gidaje Umar Ibrahim El-Yakub yay a bayyana haka, yayin da ya duba wani aikin titi a Kaduna, inda ya ce an tsaida aikin ne bayan harin da aka kai wa jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.

Tankar Mai Ta Fadi A Babban Hanyar Lagos Zuwa Ibadan

A wata sanarwa daraktar yada labarum sa Blessing Lere-Adams ta fitar, ta ce akasin abin da mutane ke cewa an yi watsi da aikin ba haka lamarin yake ba, an dakatar da aikin ne kuma za a cigaba.

 

Daraktar ma’aikar ayyuka da gidaje, ta ce ba da dadewa ba za a cigaba da aikin titin Abuja zuwa Kaduna da Kano domin an samu tsaro a halin yanzu.

 

Advertisement

Mutane da dama dai na fargabar irin wannan matakan, ka iya jawo tsaiko ne game da aikin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending