Connect with us

News

Gwamnoni uku na shirin halasta kuɗin haram a Najeriya – EFCC

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce tana sa ido kan gwamnonin ƙasar uku sakamakon yunƙurinsu na halasta kuɗin haram da biliyoyin kuɗin da suka tara ta hanyar biyan ma’aikata albashi a hannu – maimakon ta banki.

 

Advertisement

Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya faɗa wa jaridar Daily Trust cewa dakarunsa za su ci gaba da kai samame kan ‘yan canji game da zargin ɓoye dalar Amurka wanda hakan ke sa darajarta na hauhawa.

FG vs ASUU: Sabon Yajin aiki ya fara kunno kai a dalilin Albashin Oktoba

Advertisement

Duk da cewa Bawa bai faɗi sunan gwamnonin ba, ya ce biyu daga cikinsu daga arewacin Najeriya suke, inda ɗayan yake a kudanci.

 

Advertisement

Ya ce bayanan sirri da suka samu sun nuna cewa gwamnonin sun kammala shirin fito da kuɗin ta hanyar biyan ma’aikatansu na jiha da garin kuɗi maimakon ta banki kamar yadda aka saba.

 

Advertisement

“Bari ku ji, a rahoton sirri da na samu jiya…tuni wasu gwamnonin jiha da suka ɓoye garin kuɗi a gidaje yanzu suka fara ƙoƙarin biyan albashi a hannu a jihohin nasu,” in ji shi. .

 

Advertisement

Da aka tambaye shi ko EFCC za ta yi wa gwamnonin sammaci, Bawa ya ce suna dai saka musu ido zuwa yanzu.

 

Advertisement

EFCC na ɗaukar matakan ne a baya-bayan nan bayan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da shirin sake fasalin takardun naira na N200 da N500 da N1,000, inda ya ba da wa’adin kwana 47 ga ‘yan ƙasar da su kai tsofaffin banki.

 

Advertisement

Wasu masana na ganin cewa hakan na da nasaba da ƙarin karyewar darajar nairar. CBN ya ce za a fara amfani da sabbin takardun kuɗin daga ranar 15 ga watan Disamban 2022.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending