News
Yan bindiga sun kashe mutum 18 a Benue
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Akalla mutum 18 suka rasa rayukansu bayan hari da ‘yan bindiga suka kai hari a yankin Ukohol na karamar hukumar Guma da ke jihar Benue.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai bai wa shugaban karamar hukumar shawara kan harkar tsaro Christopher Waku, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin jiya Alhamis lokacin da mutane suke tsaka da cin kasuwa a yankin.
COP 27: Ambaliyar Ruwa A Najeriya, Da Wasu Ya Zama Wani Bangare Na Abun Tattaunaw
Ya kuma ce ana ci gaba da bincike domin gano wadanda suka bata.
Shi ma, shugaban karamar hukumar, Mike Ubah, ya tabattarwa manema labarai faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan bindigar sun zo ne sanye da baƙaken kaya, inda da isar su suka fara buɗewa mutane wuta a cikin kasuwar da kashe goma nan take.
Ubah ya kara da cewa sun kai wasu hare-hare a kauyuka da ke kusa tare da kashe mutum takwas.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta tabbatar da kai harin amma ta ce ba su da wasu bayanai ya zuwa yanzu.
