News
An dakatar da dan majalisa a Faransa saboda yin kalaman nuna wariya a majalisa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An dakatar da dan majalisar nan na Faransa Gregoire Fournas tsawon kwanaki 15, bayan kalamansa na nuna wariya a zauren majalisar.
Ya yi kalaman ne kan wani dan majalisa bakar fata yayin muhawara kan yan ci rani da ke tudadowa Turai.
COP 27: Ambaliyar Ruwa A Najeriya, Da Wasu Ya Zama Wani Bangare Na Abun Tattaunaw
A martanin da ya ke yi ga dan majalisar kan batun Mr Fournas yace bakaken su koma Afrika.
To amma kalaman ba su y iwa Carlos Martens Bilongo dadi ba, wanda yace a Faransa aka haife shi, a don haka bai dace wani ya nuna masa wariya ba saboda bambancin launin fata.
Sai dai, tuni ‘yan majalisa suka jefa kuriar hukunta Mr Fournas, inda aka dakatar da shi sati biyu kuma za a biya shi rabin albash
Advertisements
