News
Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Zai Dawo Aiki A Watan Nuwamba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin Tarayya ta ce za a ci gaba da sufurin jirgin kasan Abuja-Kaduna a cikin watan Nuwamba da muke ciki.
Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a yayin da yake jawabi kan ayyuka ma’akatar.
Kotu ta yanke wa su Mubarak Pikin hukuncin bulala ashirin
Ya bayyana cewa an tanadi matakan tsaro na tsawon awa 24 ga sufurin jirgin kasan, wanda wata bakwai ke nan da dakatar da shi.
Wannan na zuwa ne makonni kadan bayan Gwamnatin Tarayya ta ce ragowar fasinjojin da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a jirin kasan a watan Maris, 2022.
A watan Maris ne Gwmnatin Tarayya ta dakatar da sufurin jirgin kasan Abuja-Kaduna, bayan ’yan ta’adda sun kai masa harin bom suka kashe mutum 10 tare da sace wasu 60.
-
News7 days ago
HAWAN DABA DA KILISA :Gwamnatin Kano Ta Ce Ba Za Ta Lamunci Kalaman Tada Zaune Tsaye Ba
-
News7 days ago
An Yi Garkuwa Da Fiye Da Mutum 80 A Cikin Mako Biyu A Arewacin Nijeriya — Rahoto
-
News5 days ago
Kwankwaso Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Ci Gaba Da Marawa Sauye-Sauyen Shugaba Tinubu Baya
