Connect with us

News

Sake Fasalin Naira: Adadin Gwamnonin Da Ke Karkashin Sa Idonmu Ya Karu 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Adadin gwamnonin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ke sa ido a kan zargin karkatar da kudade ya karu, a cewar Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, Abdulrasheed Bawa.

 

Advertisement

Dangane da shirin gwamnatin tarayya na sake fasalin tsarin Naira da kuma maye gurbin ta da sabuwar Naira, shugaban EFCC ya shaida wa Daily Trust cewa bayanan sirri da hukumar ta samu ya nuna cewa gwamnoni uku sun kammala shirin shigar da kudaden a cikin tsarin ta hanyar biyan kudadensu na Albashin ma’aikatan jihar, ya kara da cewa suna sa ido sosai a kan su.

Sojoji Sun Kashe Jagororin IPOB 13

Sai dai da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Alhamis, Bawa ya ce an sanya wa karin wasu gwamnoni ido.

Advertisement

 

Sai dai ya ki bayyana sunayen wadannan gwamnonin.

Advertisement

 

Bawa ya kuma yabawa sabon aikin na sake fasalin Naira, inda ya bayyana shi a matsayin wani muhimmin tsari a yakin da ake yi da laifukan kudi da sauran nau’ukan cin hanci da rashawa a kasar nan.

Advertisement

 

A cewarsa, makudan kudaden kasar da suka bar hannun babban bankin Najeriya (CBN) ya sa bayan laifuffukan hada-hadar kudi ke da wuya.

Advertisement

 

Ya ce sake fasalin kudin Naira wata dama ce ga gwamnati ta sake farfado da harkokin kudi a kasar.

Advertisement

 

Ya bukaci ‘yan siyasa da su yi yakin neman zabe ba tare da amfani da kudaden haram ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending