News
Mutane 20 Sun Mutu A Yayin Wata Mota Ta fada Ramin Ruwa A Pakistan
DAGA KABIRU BASIRI FULATAN
Akalla mutane 20 ne suka mutu, ciki har da yara 11, a lokacin da wata karamar motar bas ta fada cikin wani rami mai zurfi da ruwa a kudancin Pakistan, in ji ‘yan sanda a ranar Juma’a.
Kasar Pakistan na da yawan mace-mace a kan tituna, inda ake zargi da lalacewa kan manyan tituna da kuma tukin ganganci.
Da yammacin jiya Alhamis a lardin Sindh, motar bas din ta fada cikin wani rami mai cike da ruwa a hanyar da ambaliyar ruwa ta tafi da ita a wannan bazarar, in ji jami’in ‘yan sanda na yankin Khadim Hussain.
“Direban bai iya ganin alamar karkatar da hanya ba don haka motar ta fada cikin wani rami mai zurfin kafa 25 (mita takwas)” kusa da garin Sehwan Sharif.
Hussain ya ce yaran da su mutum ‘yan tsakanin shekaru biyu zuwa takwas ne, mai yiwuwa suna zaune a kan cinyar iyayensu lokacin da suka samu munanan raunuka. An kuma jikkata wasu 14 a hadarin.
Pakistan ta sha fama da mamakon ruwan sama da aka yi a bana wanda ya jefa kashi uku na kasar cikin ruwa, ya raba mutane miliyan takwas da muhallansu, tare da lalata ababen more rayuwanta da tuni suka durkushe.
Bincike mai inganci ya danganta bala’in ambaliya da sauyin yanayi.
A cewar alkalumman Hukumar Lafiya ta Duniya, sama da mutane 27,000 ne aka kashe a kan hanyoyin Pakistan a cikin 2018.
AFP
