Sports
Yau za a fara gasar cin Kofin Duniya na kwallon kafa a Qatar
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Yau za a fara wasannin gasar cin kofin duniya na kwallon kafa a kasar Qatar.
Wannan shi ne karo na 22 da za a gudanar da gasar cin kofin duniya, kuma shi ne karo na farko a Gabas ta Tsakiya.
Kazalika wannan ne kuma karon farko da za a gudanar da gasar ba a watan Yuni ko Yuli ba.
Tuni dai Qatar ta tanadi filayen wasa guda takwas da za a buga wasannin, kuma za a bude wasan farko ne a filin wasa na Al Bayt, inda za a buga wasan tsakanin Qatar, mai masaukin baki, da kuma Ecuador.
Wannan kuma shi ne karo na hudu da kasashen biyu za su buga wasa a tsakaninsu.
Tawaga 32 ce za su kece raini a gasar: 13 daga nahiyar Turai, sai shida daga Asiya da Kudancin Amurka mai hudu, sai arewaci da tsakiya da kuma yankin Carebiya mai tawaga hudu sai kuma nahiyar Afirka mai biyar.
Kasar Faransa ce dai mai rike da kofin, wanda ta lashe a Rasha a 2018.
A ranar 18 ga watan Disambar 2022 ne za a kammala gasar.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
-
News5 days ago
Kwamitin Tsara Kundin Yakin Neman Zaɓen Gwamnan Kano Ya Yi Taron Tsare-tsare Manufofin Ci Gaban Jihar A Kaduna
