Connect with us

News

Ana fargabar mutuwar mutane da dama bayan da ruwa ya tafi da gidajensu

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

Ana fargabar mutane da dama sun mutu bayan ruwa yayi awon gaba da gidajensu sakamakon mamakon ruwan sama a tsiburin Ischia na ƙasar Italiya.

Advertisement

 

An ga ɓaraguzan gine-gine da bishiyoyi da kananan motoci tare da sauran tarkace ruwa na gudu da su cikin kogi a ranar Asabar.

Advertisement

Ranar Litinin Za A Dawo Da Sufurin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna – Gwamnati

Wata mace mai shekara 25 tare da iyalanta ciki har da sabon jaririnta na daga cikin waɗanda rahotonni ke cewa sun ɓace.

 

Advertisement

Magajin garin Lacco Ameno ɗaya daga cikin garuruwan da ke tsiburin, ya ce har yanzu ba a san inda gomman iyalai suke ba, yayin gine-gine da dama suka ruguje. Haka kuma rahotonni sun ce mutane da dama na maƙale a cikin wani otal da ke tsiburin.

 

Advertisement

An dai yi gargaɗin cewa yanki zai fuskanci mamakon ruwan sama haɗe da iska mai ƙarfi har zuwa ranar Lahadi.

 

Advertisement

Jami’an yankin sun umarci mazauna tsiburin da su zauna a gidajensu, domin kauce wa rashin samun taimakon gaggawa idan buƙatar hakan ta taso.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending