Connect with us

News

An Sace Fasinjoji Cikin Motar Haya A Hanyar Abuja

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

An yi garkuwa da fasinjoji da ba a san iya adadinsu ba a hanyarsu ta zuwa Abuja.

Advertisement

 

Shaidu sun ce an tare motar fasinjojin da suka taso daga yankin Kudancin Najeriya ne da bakin bindiga da yamma, aka yi cikin daji da su, a kauyen Ochadamu, wanda masu garkuwa da mutane suka addaba.

Advertisement

 

Shugabar matan jam’iyyar PDP ta sauya sheƙa zuwa APC a Yobe

Sun ce an sace fasinjojin ne daga wata motar safa mai kujeru 18 a kauyen da ke kan Babbar Hanyar Anyigbauwa Itobe a Karamar Hukumar Ofu, Jihar Kogi.

Advertisement

 

A cewarsu, a baya, ayyukan masu satar mutane sun ragu a yankin na Ochadamu amma a baya-bayan nan abin ya karu, tun bayan da wani mummunan hatsari ya sa sojoji janye shingayen bincikensu.kamar yanda aminiya ta rawaito

Advertisement

 

 

Advertisement

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro da suka hada da ’yan banga sun fara yin shara a yankin da nufin kubutar da fasinjojin.

 

Advertisement

A ranar Alhamis, Mashawarcin Gwamnan Yahaya Bello kan Tsaro, Nebi Kwamanda Jerry Omodara (murabsu), ya tababtar dafaruwar lamarin, da cewa ana kokarin ceto mutanen.

 

Advertisement

A cewarsa, gwamnatin jihar ta dauki tsauraran matakai tare da sauya fasalin tsaron jihar domin murkushe masu ayyukan laifi a yankin.

 

Advertisement

Kokarin wakilinmu na jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, SP William Aya, bai yi nasara ba, bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon ta aka tura masa ba.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending