Connect with us

News

Jigawa: Uwa da ‘Ya’yan ta Mata Biyu Sun Mutu Sakamakon Tashin Gobara

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

 

Wata uwa mai suna Khadija Ibrahim ‘yar shekara 30 da ‘ya’yanta mata biyu sun mutu a wata gobara da ta tashi a kauyen Tsangarwa da ke karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

 

 

Advertisement

Wata sanarwa da kakakin hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC, Command CSC ya fitar. Adamu Shehu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, da misalin karfe 11:00 na safe, inda gobara ta kone wata bukka a lokacin da wadanda abin ya shafa ke barci.

Mun Rufe Asibitocin Bogi Sama Da 100 A Karamar Hukuma Daya — Gwamnatin Kano

Sanarwar ta ce “Hatsarin gobarar ta lakume wata bukka da wata yarinya Khadija Ibrahim ‘yar shekara 30 ke kwana tare da ‘ya’yanta mata guda biyu, Aisha Ibrahim ‘yar shekara 4 da kuma Rabi Ibrahim ‘yar shekara 2.

 

 

 

Ya bayyana cewa duk da mahaifiyar da ‘ya’yanta mata guda biyu gobarar ta cinye gaba daya saboda babu daya daga cikin wadanda abin ya shafa da aka ceto da ransu.

Advertisement

 

 

‘’CSC Adamu ya ce ba a san musabbabin tashin gobarar ba, amma makwabta sun ce watakila ba za a rasa nasaba da wutar gawayi da ake son sanya musu dumi ba,’’ in ji sanarwar.

 

Jaridar solacebase ta ce an kai gawarwakin wadanda abin ya rutsa da su asibiti kuma likitoci sun tabbatar da mutuwar su sannan kuma aka binne su

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending