News
Mata na bore kan haramcin zuwa jami’a da Taliban ta yi
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
‘Yan mata a Afghanistan sanye da hijabi sun cika wasu titunan jami’o’insu, domin zanga-zangar kin amincewa da matakin gwamnatin Taliban na haramtawa mata zuwa Jami’a.
Saudiyya Ta Soke Gwajin COVID-19 Da Yawan Shekaru A Hajjin 2023
Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an tsaro sun hana matan wucewa tare da tasa keyarsu komawa inda suka fito.
Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa sun nuna matan na rusa kuka lokacin da jami’an tsaron suka korasu.
Watanni 16 kenan da gwamnatin Taliban ta hana mata mata ‘yan makarantar sakandare , lamarin da ya janyo damuwa ganin yadda ake yi wa ilimin mata kafar ungulu.
Wata daliba a jami’ar Kabul ta shaidawa BBC ”Sun wargaza rayuwarmu, sun wargaza gada daya tilo da ke tsakaninmu da ingantacciyar rayuwa.”
