News
Duniya Ta Yi Maraba Da Zuwan Shekara Ta 2023 Cikin Ƙayatarwa
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Ƙasashe da dama sun yi bikin tarbar sabuwar shekarar 2023 duk da yake ba a yin bikin a tare saboda lokuta da suka bambanta.
Kiribati ce ƙasar Pacific da ta fara bikin shigowar sabuwar shekarar, sai New Zealand da ta bi sahu bayan sa’a ɗaya.
Dubban mutane ne suka yi dafifi a Sydney domin kallon wasan wuta mai tartsatsi da dallare sararin samaniya cike da mabambantan launuka.
A Sydney, an harba tartsatsin wuta daga gadar Harbour da Opera House.
Haka ma abin yake a New Zealand da Koriya ta Kudu. Mutane da dama sun fita kan manyan tituna suna harba tartsatsin wuta.
Ƙasashen Afirka kamar nan Najeriya da Kenya da Uganda da Masar su ma sun yi nasu bikin shiga shekarar 2023.
Birnin London ma ya yi murnar zuwan sabuwar shekarar inda aka shafe minti 12 ana ta harba tartsatsi – abin da Magajin Birnin Sadiq Khan ya ce shi ne mafi girma a Turai.
Wannan ne karon farko da mutane suka taru a babban birnin na Birtaniya don bikin sabuwar shekara tun bayan ɓarkewar annobar korona.
A bikin murnar zuwan 2023 a London, an karrama marigayiya Sarauniya Elizabeth da ta mutu a watan Satumba.
An haska wasu alamomi na masarautar a shagulgulan da aka nuna hoton marigayiyar a kan tsabar kuɗi.
Daga bisani kuma hoton ya rikiɗe zuwa sigar Sarki Charles.
