News
Ƴan sanda a Katsina sun ce sun kashe wani gawurtaccen ɗan bindiga a jihar
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Katsina ta ce ta daƙile wani hari da aka kai Magamar Jibiya da Ƙaramar Hukumar Jibiya duk a Jihar Katsina tare da kashe wani gawurtaccen ɗan bindiga.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sanda jihar SP Gambo Isah ya fitar, ƴan sandan sun ƙwace bindiga ƙirar AK 47 guda ɗaya da ƙundun harsasai guda huɗu da ke ɗauke da harsasai 90.
Tinubu Da Atiku Sun Yi Wa Obasanjo Raddi Kan Goyon Bayan Obi
Ɗan bindigan da aka kashe sunansa Ibrahim Dangawo wanda ake zargin shi ya kitsa wani hari da aka kai har aka kashe wani tsohon DPO na Jibiya wato DSP Abdulkadir Rano.
Bbc ta rawaito cewa A jiya Litinin da misalin huɗu da rabi na yamma ne ƴan bindiga suka rinƙa harbi kan mai uwa da wabi inda suka kai hari kan wani shingen binciken ƴan sanda a Magama a kwanar Hirji a kan hanyar Jibiya.
Bayan musayar wuta da ƴan sandan suka yi da su, a nan ne ƴan sandan suka daƙile harin tare da ƙwace wasu makamansu.
Sanarwar ta ce akasarin yan bindigan da suka tsira daga harin sun tsira da raunin harbin bindiga.
