Connect with us

News

Dalilin Da Rikicin Zabe Ya Ki Ci Ya Ki Cinye Wa A Najeriya

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

 

 

Shugabar Kotunan Daukaka Kara ta Kasa Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta ce tarin matsalolin da matakan gudanar da zaben Najeriya ke da shi ne ummul’aba’isin rikice-rikicen a fannin.

 

Mai shari’a Dongban-Mense ta ce yiwuwar rikice-rikicen ce ta sanya aka kafa kotunan sauraron kararrakin zabe, don warware rigingimun zabe da dangoginsu.

Advertisement

 

Gwamnan Yobe ya bai wa ma’aikata hutun kwanaki biyu domin tarbar shugaba Buhari

 

Aminiya ta rawaito cewa Ta ce matukar ana son kawo karshen wadannan fitintinu, to dole sai an gyara tsarin zabe daidai da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da kuma Dokar Zabe ta 2022.

 

“A matsayin kotunan daukaka kara na matakin kusa da karshe a shari’a, aikinsu ne kafa irin wadannan kotunan da kuma bude wuraren rajista akalla sati daya kafin gudanar da zaben.

 

Advertisement

 

“Haka kuma alhakinsu ne kula da gudanarwar kotunan, bisa jagorancin mai mukamin sakatare”, in ji ta.

 

Ta bayyana hakan ne a jawabinta na bude taron kara wa juna sani na kwana biyu ga sakatariyar kotun zabe a jiya a Abuja.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending