Connect with us

News

Gwamnan Yobe ya bai wa ma’aikata hutun kwanaki biyu domin tarbar shugaba Buhari

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

 

Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya bai wa ma’aikata hutun kwanaki biyu wato Litinin da Talata domin ziyarar da shugaba Buhari zai kai jihar.

Advertisement

 

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar dauke da sa hannun shugaban ma’aikata na jihar, Alhaji Garba Bilal a Damaturu a ranar Lahadi.

Advertisement

 

FRSC Ta Fara Yi Wa Direbobi Gwajin Ta’ammali Da Barasa

Buhari zai ziyarci jihar domin kaddamar da wasu manyan ayyuka ciki har da tashar jirgin sama ta sauke kaya da wani katafaren kasuwar zamani da kuma cibiyar lafiya.

Advertisement

 

Gwamnati ta ce ta bada hutu ne domin ma’aikata da sauran al’umma su samu damar tarbar shugaban wanda zai kai ziyarar kwana guda a jihar.

Advertisement

 

Sai a ranar Laraba ake sa ran ma’aikata su koma bakin aikinsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending