News
Ƴan bindiga sun kai wa shugaban kwalejin fasaha Hari
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kwalejin fasaha ta jihar Osun ta tabbatar da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa shugabanta, Dr Samson Adegoke a jiya Litinin.
Kakakin kwalejin, Dr Wale Oyekanmi ne ya bayyana haka a yau Talata a garin Osogbo, inda ya ce an kai wa shugaban makarantar hari ne mintuna 10 da barinsa ofishin da misalin karfe 3:20 na yammacin ranar Litinin.
Oyekanmi ya ce maharan sun yi harbi kan motarsa a kusa da unguwar Eti-Ooni bayan yunkurin da suka yi na tare motar ta sa ya ci tura bayan da wata babbar motar dakon yashi ta kawo musu cikas.
“An yi sa’a, shugaban kwalejin ko direban sa ba wanda ya samu rauni a lokacin harin. Shugaban kwalejin na cikin koshin lafiya kuma an kai rahoton lamarin ga ƴan sanda,” inji shi.
Daily Nigeria ta rawaito Cewa Lokacin da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Osun, SP Yemisi Opalola, game da lamarin, ya ce ana ci gaba da bincike.
