Connect with us

News

’Yan Bindiga Sun Sake Kone Ofishin ’Yan Sanda A Imo

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

 

Wasu mahara sun kone ofishin ’yan sanda na yankin Afor Atta da ke Karamar Hukumar Njaba a Jihar Imo.

Advertisement

 

Wannan na zuwa sa’o’i 24 bayan wani hari da wasu ’yan-ina-da-kisa suka kai wa tsohon gwamnan jihar, Ikedi Ohakim.

Advertisement

 

Na Dawo Saudiyya Ne Domin Neman Ilimi —Ronaldo

Maharan sun jefa wasu ababen fashewa cikin ofishin ’yan sandan, lamarin da ya sanya ta kama da wuta.

Advertisement

 

A watan Yunin 2021 ma wasu bata-gari sun lalata wani sashe na wannan caji ofis tare da kone wasu kotu biyu da ke daura da ofishin ’yan sandan.

Advertisement

 

 

Advertisement

Sai dai ba a samu rahoton rauni a bangaren ’yan sanda a sakamakon harin da suka kai ba.

 

Advertisement

Aminiya ta Jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, ya ci tura sakamakon wayarsa na kashe.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending