Sports
Laifina ne rashin kokarin Haaland – Guardiola
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya dauki alhakin zargin da ake yi wa dan wasansa na gaba Erling Haaland game da rashin koarin da yake wajen cin kwallo.
Haaland ya ci kwallo 27 a duka wasannin da ya buga tun bayan baro Borussia Dortmund a wannan kakar.
Amma a wasa ukun karshe da ya buga ya gaza cin kwallo sai dai Guardiola ya ce yadda ake kai masa kwallo ne ya ragu.
“Muna da salon yadda muke buga wasa, muna da ka’idojin wasanmu amma yadda muka yi wasa a wasanni biyun karshe da muka buga, ya janyo koma baya ga Haaaland,” in ji Guardila.
Advertisements
