Connect with us

News

Daliban makaranta sun kai wa ‘yan sanda hari bayan kashe abokin karatunsu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Wasu dalibai a lardin Free State na Afirka ta Kudu sun yi wata tarzoma a ranar Alhamis bayan da labarin mutuwar wani dan makarantarsu, lamarin da yasa har suka juya wata motar ‘yan sanda har suka jrikitar da ita a gefenta.

 

Advertisement

Wani rahoton jaridar intanet mai suna Times Live, ya nuna cewa dan makarantar ya kashe kansa ne a sanadiyyar muzgunawar da wani malami ya rika yi masa.

Ana zargin wata mata da ajiye gawar mahaifiyarta kusan shekaru biyu a cikin injin daskarewa

‘Yan sandan yankin sun sanar cewa, “Dalibin ya bar wata wasika da ke cewa malamin ne yayi sanadin kashe kansa da yayi.”

Advertisement

 

Bayyanar labarin mutuwar dalibin ya sa ‘yan makarantar “su tunzura kuma suka fara lalata kayayyakin makarantar”, kamar yadda jami’in ‘yan sanda Warrant Officer Peter Mabizela ya sanar.

Advertisement

 

bbc ta rawaito cewa Daga nan ne dalibai daga makarantun da ke kusa suka tarua makarantar sakandare ta Tlotlisong, inda suka yi garkuwa da wasu ‘yan sanda biyu da malaman makarantar cikin wani daki.

Advertisement

 

Daliban sun kuma kai wa motar ‘yan sandan hari, inda suka juya ta zuwa gefenta. Sai dai aka tura karin jami’an ‘yan sanda sannan aka kwantar da tarzomar daliban.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending