News
Mutum uku sun mutu bayan faduwar gini
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Mutum uku sun mutu bayan da wani gini da ba a ƙarasa ba ya faɗi a garin Ngbodo a ƙaramar hukumar Ikwerre na jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Bbc ta rawaito cewa faduwar ginin mai hawa biyu ya yi sanadin mutuwar leburori uku da ke aikin ginin.
Harry Kane ya zama ɗan wasan da ya fi kowa zura ƙwallo a Tottenham
Babban kwamandan hukumar tsaro ta Civil Defense na jihar Michael Ogar wanda ya jagoranci jami’an hukumar wajen aikin ceto leburorin, ya danganta lamarin da rashin amfani da ingantattun kayan aikin gini.
A wata sanarwar da hukumarsa ta fitar ta ce binciken farko ya nuna cewa rodi da filoli da bulon da aka yi amfani da su wajen ginin ba su da ingancin da ake buƙata.
Faɗuwar gine-gine musamman waɗanda ba a kammala ba, ba sabon abu ba ne a Najeriya, domin kuwa ko a cikin makon da ya gabata ma wani ginin da ba a kammala ba ya fadi a Abuja babban birnin ƙasar.
