News
EFCC ta gurfanar da matar gwamnan Kogi a kotu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nijeriya, EFCC ta ce ta gurfanar da wasu makusantan gwamnan jihar Kogi a gaban kotu, ciki har da uwargidansa, Rashida Bello.
Tana zargin su ne da laifukan da suka shafi ɓarnata dukiya da halasta kuɗin haram na sama da naira biliyan uku.
Kotun Ƙolin Najeriya ta dakatar da CBN daga aiwatar da wa’adin amfani da tsofaffin kuɗi
A cewar EFCC, tuni Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ƙarƙashin Mai shari’ah Obiora Egwuatu ta ba da umarnin tsare ɗan ɗan’uwan gwamnan mai suna Ali Bello a gidan yari.
Hukumar ta ce mutanen da ta gurfanar ɗin su ne Abba Adauda da Yakubu Siyaka Adabenege da Iyada Sadat da kuma Rashida Bello wadda EFCC ta ce tana neman ta ruwa a jallo.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
