Connect with us

News

Kotu ta umarci Ganduje da ya dawo da Muhuyi

Published

on

 

 

Kotun Masana’antu ta Ƙasa da ke zamanta a Kano, a yau Litinin ta umurci gwamnatin jihar Kano da ta yi biyayya ga halin da ake ciki a da, na ayyana Muhuyi Magaji Rimingado da ta kora a matsayin shugaban hukumar yaki da cin-hanci da rashawa ta jihar, a ƙarar da ya shigar har sai ta saurari korafe-korafen sa.

 

‘Status quo ante bellum ‘yana nufin halin da ake ciki kamar yadda ya kasance kafin jayayya.

Dan wasan gaban PSG, Kylian Mbappe ya dawo atisaye bayan raunin da ya ji

An shigar da karar a gaban mai shari’a E.D. Esele, inda gwamnatin jihar Kano da majalisar dokokin jihar da kuma babban lauyan jihar Kano a matsayin wadanda ake tuhuma na 1 da na 2 da na 3.

Advertisement

 

Rimingado ya na kalubalantar sahihancin matakin da gwamnati ta dauka na korar shi ba tare da bin ka’ida ba.

 

A bisa wannan umarnin, wasikar korar da aka mika wa Mista Rimingado ba ta da wani tasiri, inda kuma hukuncin da kotun masana’antu ta kasa a Abuja ta yanke a baya ya na nan sai dai idan kotu ta yanke hukunci saɓanin wannan na baya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending