News
Abubuwa Uku da zai iya faruwa gobe a kotun koli Game Da Cigaba Da Karbar Tsoffin Kudi Ko Kuma Akasin Haka
Na farko kodai kotun ta yanke hukuncin CBN da Bankuna su cigaba da karbar tsoffin kudaden tare da cigaba da hada-hada dasu a tsakanin al-umma har zuwa lokacin da za su kare. Wannan hukuncin na iya faruwa duba da yadda wasu gwamnoni da dama suka tada hankalin su akan lallai sai an cigaba da karbar tsoffin kudaden domin siyen kuri’un talakawa da tsoffin kudaden a zabe mai zuwa.
Na biyu kodai kotun ta yanke hukuncin CBN da Bankuna su kara wasu kwanaki domin duk wani mai tsohon kudin ya samu ya kai Banki amma ba za’a cigaba da hada-hada da kudaden a tsakanin al-umma ba.
Na Uku kodai kotun ta yanke hukuncin CBN da Bankuna su daina karbar tsoffin kudaden wanda hakan zai jawo muguwar asara musamman ga ‘yan siyasa da ‘yan Kasuwar da har yanzu suka boye tsoffin kudaden wasu da niyyar su raba a lokutan zabe wasu kuma don gujewa fadawa tsadar rayuwa na rashin wadatattun sabbin kudaden.
Tun jiya Litinin wasu Bankuna da dama a Najeriya suka daina karbar tsoffin kudi saboda sunce CBN ba ta basu sanarwar su cigaba da karba ba.
Yanzu haka masu tsoffin kudade suna ta zuwa Bankunan da ake karbar tsoffin kudaden suna maidawa wanda matukar aka ce a cigaba da karbar tsoffin kudaden kuma ba’a wadata al-umma da sabbin kudin ba to tabbas wahalar da za’a kara sha sai tafi ta baya.
