News
Mutum 20 sun mutu a hadarin manyan motoci
Mutum ashirin sun rasa ransu wasu 61 kuma suka samu raunuka sakamakon wani hadarin manyan motoci biyu, bas da wata mai sulke a lardin Limpopo na Afirka ta Kudu.
Motar safa din ta fadi daga gada ta tsunduma cikin ruwa a lokacin da hadarin ya auku a jiya Litinin, kamar yadda rahotanni suka ce.
Yawancin wadanda suka mutu sun rasu ne a cikin bas din da ta fada ruwa, saboda ba ta yadda za su iya fita.
Ana gudanar da bincike kan abin da ya haddasa hadarin.
To amma rahotanni sun ce a lokacin ana ruwan sama sosai a yankin.
Har zuwa safiyar yau Talata ma’aikatan agaji suna wurin, inda ruwan sama kamar da bakin kwarya ke haifar musu cikas ga aikin nasu.
-
News1 day ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
