News
CBN Ya Sha Alwashin Hukunta masu PoS Kan Zarge-zargen Da Ya Karu Akan su
Babban bankin Najeriya (CBN) ya sha alwashin gurfanar da ma’aikatan da ke karbar makudan kudade domin hada-hadar kasuwanci.
Gwamnan babban bankin na CBN Godwin Emefiele ya bayyana haka a ranar Talata a ganawarsa da jami’an diflomasiyya.
Yayin da yake amincewa da rashin jin daɗi da manufofin sake fasalin naira ta haifar da suka haɗa da tara kuɗi da kuma tashin hankali, Emefiele ya yi alkawarin gurfanar da ma’aikatan POS waɗanda ake tuhumar su da karmar kuɗin daya wuke kayyade.
Emefiele ya yarda cewa duk da cewa wadannan lokuta ne masu wahala ga ’yan Najeriya, bai kamata a yi karin gishiri ba musamman ga masu rike da madafun iko don haifar da fargaba.
Shugaban bankin ya nanata alfanun da aka samu na sake fasalin kudin Naira, yana mai cewa ta taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma kawo daidaito a farashin canji.
Mista Emefiele ya yi kira ga mambobin jami’an diflomasiyya da ‘yan Najeriya da su amince da wannan manufa.
Ya yi nuni da cewa, duk da cewa sauya shekar zuwa rungumar sabbin takardun kudi na Naira na iya zama kalubale, amma fa’idojinsa na da yawa kuma zai haifar da tsarin rashin kudi.
