Connect with us

News

Matawalle ya kori kungiyoyi masu zaman kansu daga Zamfara

Published

on

 

 

Advertisement

Gwamnatin Jihar Zamfara ta umarci dukkanin kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a jihar su tattara su fice ba tare da bata wani lokaci ba.

 

Umarnin na cikin wata sanarwa ne da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Mamman Tsafe ya fitar.

Advertisement

CBN Ya Sha Alwashin Hukunta  masu PoS Kan Zarge-zargen Da Ya Karu Akan su 

Sanarwar ta zargi kungiyoyin wadanda ba na gwamnati ba da gudanar da ayyukan da ke iya kara matsalar tsaro a jihar da makwabta.

 

Advertisement

Gwamnatin ta ce ta lura da yadda kungiyoyin suke ta karuwa a jihar inda suke gudanar da ayyukan da suka saba wa doka.

 

Advertisement

Kuma ta ce ta lura yawancin kungiyoyin ba su yi rijista a jihar ba kamar yadda doka ta tanada.

 

Advertisement

Sanarwar ta umarci ma’aikatu da sassa da kuma hukumomin gwamnati da su daina duk wata mu’amulla da kowa ce kungiya, tare da gargadin cewa za a hukunta duk wata hukumar gwamnati da ta yi mua’mulla da kungiyoyin.

 

Advertisement

Gwamnatin ta kuma bayar da umarni ga hukumomin tsaro da su sanya ido domin gano duk wata kungiya da ke aiki ba tare da takardar izini daga hukumar da ta dace ba, domin gurfanar da ita a gaban kotu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending