News
Kwankwaso ya cinye karamar hukumar Ganduje
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, NNPP, Rabi’u Kwankwaso ya yi nasara a karamar hukumar Dawakin-Tofa, mahaifar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Kwankwaso ya doke Bola Tinubu, daya daga cikin manyan abokan hamayyarsa na jam’iyyar APC.
Da ya ke bayyana sakamakon zaben a hedikwatar INEC da ke Kano a yau Lahadi, jami’in zaɓen, Farfesa Adamu Jibril ya bayyana Kwankwaso a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 25,072
Ya kuma sanar da Tinubu na APC da kuri’u 16,773, PDP 2,477, jam’iyyar Labour ta samu kuri’u 202.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
