Connect with us

Sports

Messi na shirin buga Argentina wasa a karon farko tun bayan lashe kofin duniya a Qatar a 2022.

Published

on

 

Lionel Messi na shirin buga wa tawagar Argentina tamaula a karon farko tun bayan lashe kofin duniya a Qatar a 2022.

Advertisement

 

Argentina ta samu daukar kofin duniya na uku jimilla, bayan da ta yi nasara a kan Faransa a bugun fenariti a wasan karshe.

Advertisement

Abin da Emefiele zai fuskanta idan Buhari ya bar mulki – Shehu Sani

Koci, Lionel Scaloni ya gayyaci ‘yan wasa 35, domin buga wa Argentina wasan sada zumunta, cikinsu har da dukkan 26 da suka buga kofin duniya a Qatar.

 

Advertisement

An gayyaci Giovanni Lo Celso, wanda rauni ya hana shi zuwa Qatar da dan wasan Manchester United Alejandro Garnacho, wanda karon farko aka bashi goron gayyata.

 

Advertisement

An kuma kira wasu ‘yan kwallon a karon farko da ya hada da dan wasan Manchester City, Maximo Perrone da Facundo Buonanotte na Brighton da dan kwallon Inter Milan, Valentin Carboni.

 

Advertisement

Argentina za ta karbi bakuncin Panama ranar 23 ga watan Maris Buenos Aires asannan ta kece raini da Curacao a Santiago del Estero kwana biyar tsakani.

 

Advertisement

An yi ta rade-radin cewar Messi zai yi ritaya, bayan da dan wasan mai shekara 35 ya ja ragamar tawagar ta lashe kofin duniya a Qatar.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending