Connect with us

News

DSS Sun Kama Wasu Dauke Da Makamai A Kano 

Published

on

 

 

Advertisement

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a ranar Alhamis ta kame wasu bindigogi da aka boye a buhunnan doya a jihar Kano, ta kwamushe mutum biyu da ake zargi.

 

Advertisement

Ana zargin mutanen da dauko bindigogin ne daga wani wuri, ana kuma kyautata zaton za su wuce dasu wasu jihohin Arewa ne don aikata barna dasu.

INEC ta bai wa Ado Doguwa shaidar cin zaɓen ɗan majalisa

Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja, inda yace an kama bindigogi AK-47 guda biyu da mujallu biyu na AK-47 da babu komai a cikinsu.

Advertisement

 

A cewar Afunanya, an kuma kama buhunnan doya da wata babur mai launin ja duk dai wadanda aka boye kayan aikata laifin a cikinsu.

Advertisement

 

 

Advertisement

Ya yi kira ga masu gidajen shakatawa da wuraren wasanni da su kula sosai a lokacin bukukuwan karamar sallah da ake fuskanta,

 

Advertisement

A cewarsa: “Wannan lamarin ya nuna akwai bukatar ‘yan kasa su zuba ido sosai kuma kai rahoton duk wani bakon abu ko motsin abin zargi, mutum ko su dauki matakin kai batun ga cibiyoyin tsaro mafi kusa.

 

Advertisement

“Masu gidajen shakatawa, gidajen saukar baki da bude ido duk ana shawartarsu da su kula a lokacin bukukuwa.

 

Advertisement

“Ya kamata su dauki matakan kariya a wurarensu. Sai dai, hukumar na yiwa Musulmai fatan bikin karamar sallah cikin lumana da farin ciki.”

 

Advertisement

Hakazalika, hukumar ta ce za ta yi aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending