Connect with us

News

Bayan shekara biyu, ’yan bindiga sun sako karin daliban FGC Birnin Yauri da ke hannunsu

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

 

 

Bayan shekara biyu, ’yan bindiga sun sako hudu daga cikin ragowar daliban Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya ta ’Yanmata (FGC) da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi da ke hannunsu.

 

Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar Karamar Sallah da dare ne jagoran ’yan bindiga, Dogo Gide, ya sako karin daliban a cikin dare.

Kwamishinan Zaben Adamawa Ya Yi Layar Zana Bayan Sanar Da Sakamakon Bogi —INEC

Yaran da aka sako suna daga cikin dalibai 11 da suka rage a hannun ’yan ta’addan da Dogo Gide yake jagoranta.

Advertisement

 

Wadanda aka sako din su ne: Bilha Musa da Faiza Ahmed da Rahma Abdullahi da kuma Hafsa Murtala.

 

Shugaban kungiyar daliban da aka sace, Salim Kaoje, ya shaida mana cewa, “Sai da aka kwana shida ana tattaunawa a cikkin daji kafin aka sako mana yaran.

 

“Saura ragowar yara bakwai da wasu mutum biyu daga cikin iyaye suke cikin daji suna kokarin ganin an sako su.”

Advertisement

 

Salim Kaoje ya bayyana cewa an biya kudin kafin a sako daliban, kuma kadarorin iyayen suka sayar suka tara kudin da taimakon wasu ’yan Najeriya domin biyan kudin fansan.

 

Idan ba a manta ba a watan Janairu Kaoje ya tabbatar cewa suna tattaunawa da Dogo Gide, bayan da suka samu mahaifiyar dan ta’addan ta sa baki domin ya sako su.

 

 

Advertisement

A ranar 17 ga watan Yunin 2021 ne ’yan ta’adda suka kai hari a makarantar kwana ta FGC Birnin Yauri, mallakin Gwamnatin Tarayya, suka sace daliban.

 

Daga baya suka sako daliban, amma suka ci gaba da rike wasu guda 11, duk kuwa da cewa an biya makudan kudade da kuma musayar daliban da wasu ’yan bindiga da ke hannun gwamnati a lokuta daban-daban.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending