Connect with us

News

Hatsarin kwale-kwale ya kashe mutum biyar a Kano

Published

on

 

 

Advertisement

Akalla mutum biyar ne suka rasu sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a Jihar Kano.

 

Advertisement

Mai magana da yawun ‘yan sandan ihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar wa TRT Afrika da lamarin. Ya bayyana cewa wasu matasa takwas ne suka je kogin Panshekara inda suka hau kwale-kwale, biyar daga ciki suka rasu.

 

Advertisement

“A ranar 21 ga wata, misalin karfe bakwai da minti arba’in da biyar, wasu matasa su takwas da ‘yan unguwar Fagge da Dala suka je kogi na Panshekara inda suka hau kwale-kale.

 

Advertisement

“A yunkurin tsallaka wannan kogi, kwale-kwale ya kife da mutane bakwai a ciki wadanda suka fada cikin ruwa,” in ji SP Kiyawa.

 

Advertisement

Ya kara da cewa an yi yunkuri an ceto mutane guda biyu, sai kuma biyar aka ga gawarwakinsu.

 

Advertisement

Ya ce an kai su asibitin Murtala inda a nan aka tabbatar da sun rasu.

 

Advertisement

Haka kuma ya ce yanzu haka ana gudanar da bincike a kan wannan lamarin. Ana dai yawan samun hatsarin kwale-kwale a Kano da wasu sassa na Nijeriya. Ko a shekarun baya sai da kwale-kwale ya kife a Karamar Hukumar Bagwai da ke Kano inda kusan mutum 30 suka rasu.

 

Advertisement

Haka ma a Jihar Kebbi kwale-kwalen ya kife a kwanakin baya inda sama da mutum 100 suka rasa rayukansu.

 

Advertisement

Ana dai alakanta kifewar kwale-kwalen a Nijeriya da yawan lodi da kuma rashin kula da su kansu kwale-kwalen.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending