News
An kashe fitacciyar mawaƙiyar kasar Sudan Shaden Gardood
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An kashe ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan Sudan Shaden Gardood, a wata musayar wuta tsakanin ɓangarori biyun da ke faɗa da juna a ƙasar.
Misis Gardood ta rasa ranta ranar Juma’a a birnin Omdurman sakamakon faɗa tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF.
An Kammala Kwaso ’Yan Najeriya Da Suka Makale A Sudan —NIDCOM
Mutuwar mawaƙiyar mai shekara 37 na zuwa ne kwana guda bayan ɓangarorin da ke rikici da juna sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen wahalar da fararen hula ke fuskanta.
A cikin watan Afrilu ne dai faɗa ya ɓarke a ƙasar tsakanin ɓangarorin biyu.
Gardood dai na zaune ne a al-Hashmab, inda dakarun RSF ke ƙaruwa a ‘yan kwanakin nan.
Wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta an ga Gardoon na ɓuya tare da kiran ɗanta ya matsa daga kusa da taga domin kauce wa harsasai, yayin da ake ci gaba da luguden wuta a birnin.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
