News
Abba Kabir Ya Rushe Shugabannin Hukumar Alhazai Ta Jihar Kano Tare Da Nada Sabbi
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Ya amince da nada sabon babban sakataren hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Kano, tare da jami’ar gudanarwar hukumar.
Wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Ta baiyana cewar an nada Alhaji Yusuf Lawan a matsayin shugaban hukumar.
kasar Amurika Zata Dafawa Tinubu Baya Domin Inganta Tattalin Arziki Da Tsaro
Kazalika sanarwar ta baiyana Alhaji Laminu Rabi’u a matsayin bababban sakataren zartarwa na hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Kano, Yayin da Sheik Abbas Abubakar Daneji da Shiek Shehi Shehi Maihula da Ambasada Munir Lawan zasu kasance mambobi.
Sauran sune, Shiek Isma’il Mangu da Hajia Aishatu Munir Matawalle da Dr. Sani Ashir a matsayin mambobin hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
