Connect with us

News

Kamfanin suka gina Shaguna da Otel a filin Daula Hotel sunyi barazanar gurfanar da Gwamnatin Kano a gaban Shari’a

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Kamfanin Lamash Properties Limited da suka gina Shaguna da Otel a filin Daula Hotel sunyi barazanar gurfanar da Gwamnatin Kano a gaban Shari’a bayanda Gwamnati mai ci ta rushe ginin a karshen mako.

‘Daya daga cikin Jami’an Kamfanin Alhaji Aliyu Abubakar cikin wata Sanarwa daya rabawa manema Labarai yace zasu nemi diyyar Naira Biliyan 10 bayan rushe musu Gini ba tare da anji ba’asi daga garesu ba.

Hajjin bana:Yau za a fara jigilar alhazai a jihar Kano

Ya Kuma ce ba siyan wajen sukai ba, sun kulla yarjejeniyar aiki ta hadin Gwiwa wato PPP da Gwamnatin Kano cikin shekarar 2020 dan sake Gina Otel din me hade da Shaguna da rukunin gidaje. Wanda Kuma an Kula yarjejeniyar cewar kamfanin zai mallakawa Gwamnatin Kano rukunin Otel da suka sake ginawa Kuma tuni sunyi Hakan cikin watan Mayun daya Gabatar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending