Connect with us

News

Hukimar EFCC ta gargadi masu yin amfani da irin kayanta wurin wasan barkwanci

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta ja hankalin masu wasan barkwanci da su guji amfani da irin kayanta wurin wasan barkwancinsu.
A wata sanarwa da mai magana da yawunta Wilson Uwajeren ya fitar a ranar Litinin, hukimar ta EFCC ta ce an ja hankalinta ne kan yadda masu shirya wasannin barkwanci da fina-finai suke amfani da kaya mai dauke da tambarin hukumar ba tare da neman izini ba.

Tinubu ya janye rushe Hukumomin Gudanarwar NAFDAC da NDLEA

Hukimar ta EFCC na son sanar da jama’a cewa bai halatta a dinga amfani da kaya mai tambarinta wajen yin fna-finai ba tare da izini ba.

“A yayin da hukumar ke jin dadin yadda wasu ke son shirya fina-finai masu dauke da sakonnin irin aikin da hukumar ke yi don wayar da kan jama’a, to dole sai an fara neman izininta tare da nuna mata fitowar da za a yi da sunanta a fina-finai don ta tabbatar babu wani sako da ya saba da irin ayyukanta,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ce sashen hulda da jama’a nahukumar EFCC yana da kwarewar da zai iya aiki da masu shirya fina-finai da ke da burin hada gwiwa da hukumar wajen shirya fim ko wasannin barkwanci da nufin ilimintar da mutane, musamman matasa kan munin aikata ayyukan da suka shafi cin hanci da rashawa.

Advertisement

A karshe hukumar ta ce duk wanda aka kama da laifin yin gaban kansa wajen shriya fim ko barkwanci ba tare da izinin hukimar EFCC din ba, to za a dauki mataki a kansa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending