News
Kotun Legas ta wanke wata mata da ake zargi da kai wa ‘yan sanda hari
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wata mata ‘yar shekara 33 mai suna Olufumilayo Eriolowa, wadda aka tsare a gidan yari na Kirikiri bisa zarginta da yi wa wani jami’in ‘yan sanda, Olufowobi Nureni, a yankin Ogombo da ke jihar Legas, ta samu ‘yanci daga dukkan tuhumar da ake mata.
Eriolowa, wanda aka tsare a gidan yari tun ranar 17 ga watan Mayun 2023, alkalin kotun majistare M. O. Alao na kotun majistare da ke Eti-Osa, Legas, ya sake ta bayan an yi shari’ar.
Kamfanin UK ENTERTAINMENT Ya Shirya Sabon Fim Mai Dogon Zango Mai suna FATAKE
jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana cewa an tsare ta ne bisa zargin cin zarafin wani dan sanda a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wani wuri a Ogombo a jiya, ta ci zarafin wani dan sanda.
An gurfanar da ita a yau, kuma an tasa keyar ta zuwa gidan gyaran hali na Kirikiri har zuwa ranar 6 ga watan Yuni idan shari’ar ta sake zuwa kotu.”
Tun da farko dai, mai gyaran gashi ya gurfana a gaban majistare M. O. Alao bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka shafi cin zarafi da kin kama shi a kotun majistare da ke Legas, Eti-Osa.
